Isa ga babban shafi
Najeriya - Tsaro

Tsarin mulki bai baiwa Buhari ikon amfani da karfi kan 'yan aware ba - Falana

Fitaccen lauyan Najeriya kuma mai rajin kare hakkin bil’adama (SAN), Femi Falana, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da masu neman ballewa da sauran masu tayar da zaune tsaye a duk fadin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2 ga watan Yuni 2021
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, 2 ga watan Yuni 2021 Ludovic MARIN POOL/AFP/File
Talla

Falana wanda ya bayyana haka yayin jawabi wajen taron kan cin hanci da rashawa, da aka shirya saboda ranar Demokradiya, Ya nuna adawa da umarnin gwamnatin tarayya na fito-na-fito da bata garen ko bude musu wuta, musamman a yankin Kudu Maso Gabas.

Yana mai cewa gwamnati ba ta da ikon shelanta yaki a kowane bangare na kasar ba tare da bin hanyar Majalisar Dokoki ta Kasa ba kamar yadda sashi na 304 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.

Shirin, wanda aka shirya  tunawa da ranar dimokradiyya ta kasar, ya samu tallafi daga Gidauniyar MacArthur da Open Society Initiative for West Africa (OSIWA), da sauransu.

Babban lauyan ya ce duk da cewa babu wani dan Najeriya da zai goyi bayan tawayen yankin Kudu maso Gabas, amma ba daidai ba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana yaki a kan mutanen yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.