Isa ga babban shafi
Najeriya

Jama'a na da hakkin zanga-zanga kan matsalolin tsaro - Falana

Fitaccen lauya mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya Femi Falana mai mukamin SAN, ya ce gwamnatin kasar ba ta da karfin ikon haramtawa jama’a gudanar da zanga-zangar neman sauya manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasar ba, saboda gazawarsu wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Najeriya a Abuja. 9/2/2017.
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Najeriya a Abuja. 9/2/2017. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Fitaccen lauyan ya bayyana haka ne a karshen mako, yayin maida martani ga kakakin shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, wanda ya zargi jam’iyyar adawa ta PDP da yin hayar mutane kimanin dubu 2, don yin zanga-zangar neman korar manyan hafsoshin tsaron kasar, da kuma kunyata shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan na zuwa ne a daidain lokacin da al'ummar Najeriya ke fatan ganin shugaban kasar ya sauya hafsoshin tsaron kasar saboda suna ganin sun gaza wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa musamman a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikicin Boko Haram.

Sai dai yayin bayyana shirin wasu daga cikin ‘yan adawar, Garba Shehu yayi gargadin cewa gwamnati ba za ta kyale wasu tsiraru su tayar da zaune tsaye ba, da sunan zanga-zangar kyamar shugabannin rundunonin tsaro.

Sai dai yayinda yake raddi kan kalaman na garba Shehu, fitaccen lauya Falana ya bukaci tunawa da lokacin da watan Nuwamban shekarar 2014, lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, dawasu shugabannin jam’iyyar APC ciki har da jagoranta Cif Oyegun da kuma Rotimi Amechi ministan sufuri na yanzu, suka jagoranci zanga-zangar kokawa kan tabarbarewar sha’anin tsaro karkashin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.