Isa ga babban shafi
Najeriya

Hare-haren 'yan bindiga sun dakushe nasarorin Buhari - Soyinka

Masanin adabi a Najeriya farfesa Wole Soyinka, ya ce matsalolin tsaron da ake addabar yan kasar musamman hare-haren ‘yan bindiga, sun dakushe nasarorin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Farfesa Wole Soyinka.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Farfesa Wole Soyinka. Premium Times Nigeria/Bayo Omoboriowo
Talla

Soyinka ya bayyana hakane yayin kokawa bisa karuwar hare-haren yan bindiga da ake dangantawa da makiyaya sassan Najeriya, wanda a yanzu ya bazu zuwa kudancin kasar, inda a baya bayan nan wani gungun ‘yan bindigar da ake zargin makiyayan ne suka halaka Funke Olakunrin, ‘ya ga Pa Reuben Fasorantin shugaban kungiyar Afenifere mai kare muradun Yarbawa zalla a Najeriya, yayin da take kan hanyar zuwa Legas daga Akure.

Kisan dai ya haifar da muhawara mai zafi daga bangarori da dama.

Yayinda tsokaci kan halin da tsaro ke ciki a Najeriya, farfesa Soyinka ya zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen daukar matakan da suka dace don kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da ke yawaita, lamarin da yace ya yi sanadin salwantar rayukan ‘yan Najeriya masu yawan gaske.

Farfesan ya kara da cewa, sha’anin tafiyar da mulkin Najeriya yana da matukar wahala, la’akari da tarihin kafuwarta, ginshikan da suka kafa kasar, siyasa da kuma al’adu.

Masanin adabin da ya cika shekaru 85, ya kuma zargi yan siyasar kasar da fifita neman kudi ta kowane hali fiya da bukatun talakawa, matsalar da ya ce ta haifar musu da dimuwa da rashin fahimtar nauyin da ya rataya a wuyansu.

Domin samar da mafita ga matsalolin, farfesa Soyinka ya shawarci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci taron kasa tsakanin dattawa, shugabannin addinai, kabilu, sarakunan gargajiya, ‘yan siyasa, jami’an tsaro, dasauran masu ruwa da tsaki domin yiwa matsalolin Najeriya dibar karan mahaukaciya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.