Isa ga babban shafi
Najeriya

Tsokacin masana kan sabuwar wasikar Obasanjo

Kalubalen da Najeriya ke fuskanta daga bangarori daban daban na ci gaba da haifar da muhawara kan gazawa da kuma kokarin hukumomin kasar wajen kawo karshen matsalolin da ke ci wa jama'a tuwo a kwarya, musamman sha’anin tsaro.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo. REUTERS/Joe Penney
Talla

A baya bayan nan dai hare-haren ‘yan bindiga da wasu ke dangantawa da makiyaya shi ne babban al’amarin da yan Najeriya ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu akai, ciki harda wasu tsaffin shugabannin kasar, masana, jagororin addini, ‘yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Wasu bangarori dai na kallon matsalar tsaron ta hare-haren ‘yan bindiga a matsayin gazawar gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kamar yadda a farkon makon nan masanin adabi a kasar Farfesa Wole Soyinka ya bayyana, a lokacin da yake tsokaci kan halin da tsaro ke ciki.

Sa’a’o’i bayan tsokacin na Soyinka ne kuma, tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya rubuta budaddiyar wasika ga shugaban kasar Muhammadu Buhari, inda ya gargade shi da ya gaggauta daukar matakan ceto kasar wanda yanzu ta kama hanyar tabarbarewa saboda matsalolin tsaro dake haifar da rasa dimbin rayuka.

Cikin wasikar, Obasanjo yace lokaci na kurewa yayinda al’ummar kasar ke ci gaba da bayyana korafinsu daga kowanne bangare.

Obasanjo ya bayyana wasu abubuwa 4 da yace suna damunsa da suka hada da barin kasar a hannun masu aikata laifi da ake danganta su da Fulani da Boko Haram, da shirin ramuwa kan Fulani daga wadanda aka kaiwa hari, hari kan wata kabila da ke iya haifar da ramuwar gayya, da kuma bore daga wani sashi na kasa.

Dakta Saleh Muhammed Kanam na Jami’ar Jihar Bauchi da ke tarayyar Najeriya, na daya daga cikin masanan da suka yi tsokaci kan budaddiyar wasikar tsohon shugaba Obasanjo.

Yayin tattaunawa da sashin Hausa na RFI, Dakta Kanam ya ce Obasanjo na kokarin wanke kansa ne daga katobarar da yayi a ‘yan kwanakin da suka gabata, na bayyana zargin cewa, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kokarin Musuluntar da Najeriya tare dai maida kasar karkashin ikon Fulani, zargin da a waccan lokacin ya jawowa tsohon shugaban suka daga bangarori da dama.

Dangane da batun korafi kan gazawar gwamnati kuwa, Dakta Kanam, ya zargi gwamnatocin jihohi musamman na arewacin Najeriya da gazawa wajen hada kai, da kuma daukar matakan da suka dace a matakin farko wajen magance matsalolin da al’ummominsu ke ciki.

A cewar Daktan, gazawar gwamnonin a fannoni daban-daban ya sa hankula suka koma kan gwamnatin tarayya, abinda yace ba shi ne ya dace ba.

01:36

Dakta Saleh Kanam kan sabuwar wasikar Obasanjo

Bashir Ibrahim Idris

Yan Najeriya dai na ci gaba da muhawara kan wasikar tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, inda wasu ke goyon bayan abubuwan daya zayyana cikin, tare da bukatar ganin an sauraresu da kunnen basira, yayinda a gefe guda wasu ke kallon wasikar a matsayin yunkuri na haifar da kace-nace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.