Isa ga babban shafi
Najeriya - Siyasa

Buhari ya sake ganawa da manema labarai karo na 2 cikin mako 1

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake gabatar da jawabai kan batutuwa da dama kan halin da kasar ke ciki, yayin wata zantawa da yayi da gidan talabijin din kasar na NTA.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Nigeria Presidency/Handout via REUTERS
Talla

Karo na 2 kenan da shugaban ke bayyana a hira da manema labarai cikin mako guda, bayan da a Alhamis din da ta gabata gidan talabijin na Arise ya watsa hirar da yayi shugaba Najeriyar.

Yayin tattaunawar ta baya bayan nan, Buhari ya tabo batutuwa dama da suka shafi tsaro, da tattalin arziki da kuma siyasa.

Daga cikin abubuwan da suka ja hankali a bangaren siyasa a yayin hirar da yayi da NTA akwai fatan da shugaban Najeriyar yayi na ganin jam’iyyarsa ta APC ta ci gaba da mulkin kasar na tsawon lokaci a nan gaba, tare da shan alwashin mikawa sabuwar gwamnati mulkin kasar a cikin yanayi mai kyawu bayan gudanar zaben shekarar 2023.

Yau dai take ranar Dimkoradiyya a Najeriyar, wadda shugaba Buhari ya ware don tunawa da zaben ranar 12 ga  watan Yunin 1993 da gwamnatin sojin waccan lokaci ta soke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.