Isa ga babban shafi
Najeriya - Siyasa

Shugabannin Yarbawa na APC sun yi Allah-wadai da masu neman raba Najeriya

Shugabannin Yankin Kudu maso Yammacin Najeriya dake Jam’iyyar APC mai mulkin kasar sun yi Allah wadai da masu fafutukar ganin an raba Najeriya, yayin da suka bukaci masu irin wannan fafutuka da su gaggauta kawo karshen sa ta hanyar daina kalamun batunci domin tabbatar da cigaba da dorewar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa guda.

Shugabannin yankin kudu maso yammacin Najeriya na jam'iyyar APC bayan taron da suka gudanar kan makomar Najeriya a birnin Legas.
Shugabannin yankin kudu maso yammacin Najeriya na jam'iyyar APC bayan taron da suka gudanar kan makomar Najeriya a birnin Legas. © Western Post Nigeria
Talla

Bayan wani taro da suka gudanar a birnin Lagos wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki dake Yankin da suka hada da Chief Bola Ahmed Tinubu da Gwamnoni da shugaban Majalisar wakilai da Yan Majalisun tarayya, shugabannin sun bayyana damuwar su kan matsalolin tsaron da suka addai Najeriya, bayan sun jajantawa shugaban kasa da jama’ar Najeriya kan rasuwar shugaban sojin kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da ‘yan tawagar sa.

Shugabannin sun ce ayyukan ta’addanci da aikata manyan laifuffuka na yiwa yankuna da dama barazana ganin yadda yake shafar harkokin rayuwar jama’a, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta cigaba da kashe kudade ta hanyar zasu amfani jama’ar kasa da kuma bada isassun kudade ga sojoji da sauran jami’an tsaro domin shawo kan matsalolin da suka addabi kasar.

"Ya zama dole a kawar da kabilanci da nuna bambancin addini a Najeriya"

Sanarwar bayan taron yace, kafin Najeriya ta samu nasarar shawo kan wadannan matsaloli ya zama wajibi a samun hadin kai domin cimma muradun da aka sa a gaba da zummar samar da zaman lafiya da cigaban jama’a ba tare da banbancin addini ko kabila ba.

Shugabannin sun nuna danuwa kan yadda fitattun mutane ke kalamun tada hankali dake zagon kasa ga shirin zaman lafiya, inda suka bukaci gwamnatoci a kowanne matakai da jami’an tsaro da suyi abinda ya dace wajen ganin magance duk wata barakar da zata haifar da tashin hankali.

Sanarwar ta bukaci yan Najeriya na gari da su dinga kalaman da zasu hada kann jama’a da kuma kawar da banbance banbance, yayin da shugabannin suka yi watsi da duk wani yunkuri na amfani da karfi domin cimma manufar siyasa daga kowacce kabila ko addini ko kuma shiya, inda suka bukaci gwamnati da tayi duk abinda ya dace domin kare lafiyar wadanda ake kaiwa hari da kuma taimakawa wadanda aka ci zarafin su ta hanyar ayyukan ta’addanci ko Yan bindiga.

Shugabannin sun kuma jaddada matsayar su na goyan bayan rage ikon gwamnatin tarayya domin karfafa jihohi wajen tafiyar da mulki domin inganta rayuwar mutanen karkara.

Taron shugabannin kuma ya bayyana goyan bayan sa ga matsayar gwamnonin kudancin Najeriya na hana tafiye tafiyen kiwo da bukatar killace makiyaya da dabbobin su, inda suka bukaci babban bankin Najeriya da ya samar da tallafi ga manoma da makiyaya domin ganin sun inganta sana’oin su ba tare da samun tashin hankali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.