Isa ga babban shafi
Najeriya - Hakkin dan Adam

Kungiyoyi 127 sun bukaci Buhari ya kawo karshen rashin tsaro ko yayi murabus

Akalla Kungiyoyin fararen hula 127 dake Najeriya ne suka bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta kawo karshen kashe kashe da zub da jinin da ake samu a kasar ko kuma ya sauka daga mukamin sa domin ceto kasar daga rugujewa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin jawabin kan bikin tunawa da ranar samun 'yancin kan Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin jawabin kan bikin tunawa da ranar samun 'yancin kan Najeriya © Nigeria/presidency
Talla

Wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyoyin suka sanya hannu tace a watanni 3 na farkon wannan shekara Najeriya ta ga tashin hankalin da ta dade bata gani ba wajen kai hare hare da kashe kashe da garkuwa da mutane da kai hari kan Yan sanda da kuma sace makamai, abinda yayi sanadiyar kashe akalla mutane 2,000.

Kungiyoyin sun ce abin takaici ne halin da kasar ta samu kan ta a yau na rashin kwanciyar hankali daga kowanne bangare, inda ta bayyana shirin daukar mataki daga ranar 26 ga wannan wata da suka hada da ranar zaman makoki kan mutanen da suka mutu ranar 28 ga wata da kuma kauracewa duk wasu bukukuwan da suka shafi ranar dimokiradiya.

Kungiyoyin sun ce abin takaici ne tun bayan sanarwar da suka yi ta farko kan tabarbarewar tsaro da kuma zubda jinin da ake samu a Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari dake rike da mukamin Babban Kwamandan hafsan sojin Najeriya ya kasa daukar matakin kawo karshen matsalar, saboda haka yanzu babu abinda ya rage musu sai daukar matakin da ya rage musu.

Daga cikin kungiyoyin da suka rattaba hannu cikin sanarwar sun hada da ‘DoNigeriaRight’ da ‘Action Aid’ da ‘Baobab for Women’s Human Rights’ da ‘Bimbo Odukoya Foundation’ da ‘Centre for Democracy and Development’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.