Isa ga babban shafi

Najeriya - Masu garkuwa da fasinjojin jirgin kasa sun yi barazanar sace Buhari

A Najeriya, ‘Yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris sun fitar da sabon bidiyo inda aka nuna yadda suke azabtar da fasinjojin.

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP
Talla

Bidiyon, mai tsawon mintuna 10.52, ya nuna ‘yan bindigar ke lakada wa fasinjojin duka, yayin da su kuma Mazan su da Mata suke  kururuwa.

A cikin bidiyon mai matukar tayar da hankali, an ji wani muryar dake umurtan daya daga cikin wadanda ke lakadawa fasinjojin duka mai suna ‘”Ali da su tsayar da dukan ya isa”

Gazawar gwamnatin Najeriya

Daya daga cikin fasinjojin ya bayyana gazawar gwamnatin Najeriya, inda ya yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya irin su Amurka da Ingila da Faransa da Saudiya su taimaka su ceto su.

Bidiyon da ya karade kafofin sada zumunta ya nuno wani dan bindiga yana bayyana cewa gwamnati ce ta janwo wa mutanen wulakanci sakamakon rashin aiwatar da bukatar su.

Ya ce

“mun sani cewa kokarinku shi ne ku karbe su da karin tuwo…ku sani wannan kadan ne daga abin da za mu yi. Kamar yadda muka fada muku a baya idan har ba ku yi gaggawar aiwatar da abin da muke buka ta ba, nan wurin zai zama mayanka.”

Zamu sace Buhari da El-Rufa'i

Ya yi barazanar sace manya-manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa, ciki har da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Mataimakinsa da kuma gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’I da sanatoci har da kansiloli.

Hari kan ayarin motocin Buhari

Hakan na zuwa ne makonni kadan bayan harin da aka kaiwa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina, inda Mutane biyu suka samu raunuka a harin, wanda fadar shugaban kasar ta ce an dakile.

Harin Kuje

Harin da aka kai wa ayarin motocin ya faru ne a ranar da ‘yan ta’addar dake da’awar kafa daular musulunci a yankin yammacin Afirka (ISWAP) suka mamaye gidan yarin Kuje da ke Abuja tare da kubutar da fursunoni sama da 800 da suka hada da daukacin ‘yan ta’addan da ake tsare da su.

Ko a cikin sabon faifan bidiyo wani ya bayyana kansa amatsayin wanda ya kubuta a harin na Kuje.

Cinikin Bayi

‘Yan ta’addan sun kuma yi alfahari da cewa za su ruguza Najeriya, su kashe sauran fasinjojin da ke hannunsu sannan su sayar da sauran.

An sako wasu fasinjojin ne bayan da aka ce sun biya Naira miliyan 100 kowannen su.

Ya ci gaba da cewa a cikin harshen Hausa: “Kamar yadda ’yan matan Chibok da aka sayar, za mu sayar da wadannan a matsayin bayi. Idan ba ku bi bukatunmu ba, za mu kashe wadanda muke bukata mu sayar da sauran. Da yardar Allah, El-Rufai, Buhari, za mu kawo ka nan.”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.