Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kai hari kan tawagar motocin shugaban Najeriya

‘Yan bindiga sun kai hari kan tawagar motocin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a yayin da suke kan hanyar zuwa garin Daura a jihar Katsina, inda ake sa ran zai je domin hutun Sallar layya.

Hare-haren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya
Hare-haren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya Jakarta Globe
Talla

Bayanai sun ce tawagar da ‘yan ta’addan suka budewa wuta na dauke ne da kashin farko na jami’an tsaron fadar shugaban kasa da suka hada da na hukumar DSS, ‘yan sanda, da sojoji, da kuma ‘yan jaridu, a lokacin da lamarin ya auku.

Rahotanni sun ce mutane biyu aka tabbatar da jikkatarsu, yayinda wasu kuma ke cewa mutanen biyu rayukansu suka rasa a harin da aka kaiwa tawagar da shugaban Najeriyar ba ya cikinta a yankin Dutsinma dake jihar Katsina.

Wasu majiyoyi kuma sun ruwaito cewar, an kai harin kwanton Baunar ne sa’o’i bayan kashe wani babban jami’an ‘yan sanda da wani karamin jami’in da ‘yan bindiga suka yi a dai yankin na Dutsinma.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito wani shaidar gani da ido dake bayanin cewar kiris ya rage tashin hankalin ya rutsa da su, amma suka boyewa maharan bayan da suka kusa cin karo da jerin gwanonsu akan Babura dauke da muggan makamai.

Majiyar ta kara da cewar bayan isowar tawagar motocin fadar shugaban Najeriyar ne aka fara musayar wuta a tsakanin bangarorin biyu, daga bisani ne kuma jami’an tsaron suka tarwatsa ‘yan ta’addan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.