Isa ga babban shafi

Zamfara ta fara horas da jami'an tsaron sa-kai don dakile 'yan bindiga

Gwamnatin Zamfara ta kaddamar da shirin horas da sabbin zaratan jami’an tsaron sa-kai da ta dauka domin dakile hare-haren ‘yan bindiga a karkashin kungiyar CPG a takaice.

Jami'an tsaron sa-kai na CPG a jihar Zamfara dake Najeriya.
Jami'an tsaron sa-kai na CPG a jihar Zamfara dake Najeriya. © Daily Trust
Talla

Bayanai na nuni da cewa an zabo jami'an tsaron na CPG ne daga dukkanin masarautu 19 dake fadin jihar.

Yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da aikin horas da sabbin jami'an tsaron Gwamna Bello Matawalle ya sha alwashin aiwatar da karin matakan yaki da ta’addanci a jiharsa, la’akari da mummunan halin da ‘yan bindiga suka jefa dubban mutane musamman a yankunan karkara.

A makon da ya gabata gwamnatin Zamfara ta sanar da yanke shawarar baiwa al’ummar jihar damar mallakar bindigogi domin kare kansu daga ta’addancin ‘yan bindiga.

Zamfara dake kan gaba a tsakanin jihohin arewacin Najeriya masu fama da hare-haren ‘yan bindiga, a baya mahukuntan jihar sun sha yunkurin kulla yarjejeniyar sulhu da ‘yan ta’addan, amma lamarin ya ci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.