Isa ga babban shafi

Zamfara ta amince da hukuncin kisa kan ‘yan bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara dake Najeriya ta sanya hannu akan dokar hukuncin kisa ga duk wani dan bindigar da aka samu da laifi a jihar, yayin da aka tanadi hukuncin daurin shekaru 20 akan masu taimaka musu da bayanai.

Bello-Matawalle, Zamfara state Governor in Nigeria
Bello-Matawalle, Zamfara state Governor in Nigeria © Premiumtimes
Talla

Gwamna Bello Matawalle ya rattaba hannu akan wannan sabuwar doka wadda ake sarai ta taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka mamaye jihar, kuma suke ci gaba da daukar rayuka ba tare da kaukautawa ba.

Sabuwar dokar na zuwa ne kwana biyu bayan gwamnatin Zamfara ta umurci jama’a da su mallaki bindigogi domin kare kan su daga Yan bindigar da suka hana su zaman lafiya.

Sanarwar gwamnatin tace zata taimakawa jama’a daga Masarautun Jihar daban daban wajen ganin sun samu izini daga kwamishinan Yan Sanda domin samar musu da bindigar.

Gwamnatin tace zata taimakawa jama’a wajen mallakar bindigar bayan tantance su da jami’an tsaro za suyi domin tabbatar da ingancin halayen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.