Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe sama da mutane 50 a Zamfara

Akalla mutane 56 suka mutu a jihar Zamfara dake Najeriya, sakamakon wani hari da ‘yan biondiga suka kai wasu kauyuka uku a karamar hukumar Bakura ta jihar.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Wani tsohon kansilan da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar Premium Times ‘yan bindigar sun kai hari a Sabon Garin Damri, na kauyukan da misalin karfe 2:30 na ranar Jumma’a.

Ya ce ‘yan bindigar sun kai hare-haren ne da ake ganin kamar na bai daya a Sabon Garin Damri da Damri da Kalahe kafin rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro su tunkare su.

Wani mazaunin garin Mu’azu Damri ya ce da adadin wadanda suka mutu zai fi haka idan jami’an tsaro ba su tunkari ‘yan bindigar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.