Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Mutanen da 'yan bindiga suka kashe da rana tsaka a Zamfara sun kai 17

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 17 a wasu hare hare da suka kai kauyuka 4 a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kuma yi awon gaba da dimbim dabbobi bayan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

 

Majiyoyi daga yakin sun shaida wa shashen Hausa na RFI cewa maharan sun kutsa Kauyukan  Kadaddaba da Rafin Gero na karamar hukumar Anka ta Zamfarar, inda suka tarwatsa al’umma ba tare da samun wani kalubale daga jami’an tsaro ba.

Wata majiya ta ce tun da tsakar ranar Alhamis ne ‘yan bindigar suka fara afka wa mutane, har ma suka shiga  kasuwar  Rafin Gero da ke ci, suka yi awon gaba da dimbin shanu da rakuma da sauran dabbobi.

Mazuna yankin sun ce duk da cewa mutane sun ruga cikin daji don neman tsira, ‘yan bindigar sun yi ta bin su a kan babura suna harbewa.

Ya zuwa lokacin hada wannan labari, babu wani karin bayani daga rundunar 'yan sandan  jihar Zamfara, kuma duk kokarin samun kakainta  ya ci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.