Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace wani jami'in kwastan a Zamfara

‘Yan bindiga da ake zargi sun fito ne daga tungar kasurgumin dan bingan nan Ada Aleru sun sace wani jami’in kwastan, a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a Najeriya.

Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga.
Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga. © PHOTO/FOTOSEARCH
Talla

‘Yan bindigan wadanda yawansu ya kai kimanin 50 sun kutsa shelkwatar karamar hukumar ce da safiyar Juma’a, inda suka yi awon gaba da jami’in kwastan din, Mahassana Lawali.

Lawali, wanda akanta ne a hukumar kwastan, shiyyar Kano da Jigawa ya tafi Tsafe ne don yin hutun karshen mako tare da iyalinsa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa barayin dajin sun yi wa gidan jami’in kwastan din kawanya ne a lokacin da suke gudanar da danyen aikin nasu.

Sun ci gaba da cewa tun da farko ‘yan bindigan sun kama wani mutum, har ma suka daure shi tamau, amma suka kwance shi ya yi tafiyarsa bayan da suka fitar da jami’in kwastan din da suka kama.

‘Yan bindiga dai su na ci gaba da gudana da danyen aikinsu a yankuna da dama na arewa maso yammacin Najeriya, inda akasari suke satar mutane, dabbobi tare da yi wa mata fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.