Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun shafe sa'o'i suna ta'asa a kauyukan Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara a Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun afka wa wasu yankunan jihar, inda suka yi awon gaba da dimbin dabbobi tare da harbi kan mai uwa da wabi.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Majiyoyi daga yakin sun shaida wa shashenHausa na RFI cewa maharan sun kutsa Kauyukan  Kadaddaba da Ruwan Gero na karamar hukumar Anka ta Zamfarar, inda suka tarwatsa al’umma ba tare da samun wani kalubale daga jami’an tsaro ba.

Wata majiya ta ce tun da tsakar ranar jiya Alhamis ne ‘yan bindigar suka fara afka wa mutane, har ma suka shiga  kasuwar  Ruwan Gero da ke ci, suka yi awon gaba da dimbin shanu da rakuma da sauran dabbobi.

Kokarin kai wa ga rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara don karin bayani a kan wannan lamari ya ci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.