Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Kasurgumin dan bindiga yana neman sulhu da al'ummomin Zamfara

A Najeriya wani kasurgumin dan bindiga ya tuntubi tdattawa da masu shiga tsakani  don su taimaka wajen cimma sulhu tsakanin sa da al’ummomin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Dan bindigar mai suna Ado Alieru, ya aiwatar da hare hare da dama a kan al’ummomin da ke kananan hukumomin Tsafe ta jihar Zamfara da Faskari da ke jihar Katsina.

Sai dai wata majiyar tsaro ta ce matakin  na dan Aleiru, wata dabara ce  da ya bullo da ita don kare ‘yan uwansa da dukiyar da ya tara ta wajen aikin assha.

Jaridar  ‘Dily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa a shekarar 2020, bayan wani mummunan harin da ya kai a kauyen Kadisau ne rundunar ‘yan sandan jihar katsina ta yi alkawarin bai wa duk wanda ya kamo shi ko ya yi sanadin kama shi tukuicin Naira miliyan 5.

Babu tabbacin ko akwai hannun wata hukumar tsaro ta kasar a  cikin wannan yunkuri na sulhu da Aleiru yake shirin yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.