Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara-'Yan bindiga

Mazauna yankunan Zamfara na ci gaba da barin gidajensu saboda 'yan bindiga

Daruruwan mazauna kauyukan Magazu da  Marke, a   karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a arewa maso gabashin Najeriya ne suka tsere daga gidajensu sakamakon yadda ‘yan ta’adda da aka fi sani da ‘yan bindiga suka zafafa kai musu hare hare.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Mazauna yankuna sun ce Magazu, wanda shine mazaba mafi girma a karamar hukumar Tsafe, ya kasance kusan babu kowa a halin da ake ciki.

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito wasu majiyoyi na cewa al’ummomin wadannan yankunan sun gaji da hare hare da ake kai musu ba kakkautawa, lamarin da ya sa suka fara barin gidajensu tun daga yammacin Alhamis.

Hare haren ‘yan bindiga sun fi yin kamari a karamar hukumar Tsafe idan aka kwatanta da saura yankunan jihar Zamfara, wadda rashin tsaro ya yi mata dabaibayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.