Isa ga babban shafi

Gwamnatin Zamfara ta sauke sarakuna saboda ta'addanci

Gwamnatin Jihar Zamfara da Najeriya ta sanar da sauke manyan Sarakunan Jihar guda biyu da Magajin Gari guda saboda samun su da hannu wajen ayyukan ta’addancin da suka addabe ta.

Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle, a cikin ofishinsa dake jihar
Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle, a cikin ofishinsa dake jihar © Governor Matawalle
Talla

Sanarwar da Gwamnan Jihar Bello Matawalle ya gabatar tace an Sauke Sarkin Zurmi Atiku Abubakar da na Dansadau Hussaini Umar saboda yadda rahotan binciken da akayi ya tabbatar da laifi akan su.

Sanarwar dake dauke da sanya hannu Zailani Bappa, mai magana da yawun gwamnan tace an kuma sauke Suleiman Ibrahim Danyabi a matsayin Magajin Garin Birni Tsaba.

Sanarwar tace an dauki matakin sauke Sarakunan ne bayan taron majalisar zartarwa wanda Mukaddashin Gwamnan Jihar Hassan Nasiha ya jagoranta wanda ya amince da shawarwarin wani kwamitin bincike da ya gano hannun wadannan Sarakuna cikin matsalar tsaron da ta addabi jihar.

Kafin dai wannan lokaci an dakatar da wadannan Sarakunan daga aiki saboda zargin da ake musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.