Isa ga babban shafi

Gwamnatin Zamfara za ta bai wa mutane izinin mallakar bindiga

Gwamnatin Zamfara ta sanar da yanke shawarar baiwa al’ummar jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga hare-haren 'yan ta'adda.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai mai dauki da sa hannun kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara, gwamnatin Zamfara ta ce ofishin  kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ne zai tantance mutanen da suka cancai mallakar bindigogin don kare kansu, musamman manoma dake a yakunan karkara.

Sanarwar ta kara da cewa za a kafa cibiyar tattara bayanan sirri kan ayyukan masu taimakawa ‘yan bindiga da bayanai.

Gwamnatin Zamfaran ta kuma umarci majalisar dokokin Jihar da ta gaggauta nazartar dokar hukunci mai tsauri kan duk wanda aka kama da laifin taimakawa ‘yan ta’adda da bayanai.

Daga karshe ta kuma gargadi mutane da su tabbatar da gaskiyar dukkanin wasu bayanai da za su gabatarwa gwamnati kan wadanda suke zargi da atimakawa ‘yan bindiga, domin kaucewa tafka kura-kurai.

Zalika duk mutumin da ya ba da bayanan da ba sahihai ba kan wani, to fa za a yi masa hukunci iri daya tare da maitaimkawa ‘yan bindiga da bayanai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.