Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kai hari kan wani filin hakar ma'adinai a Neja

Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya sun ce, ‘yan ta’adda sun kashe mutane fiye da 10 cikinsu har da jami'an tsaro da ma'aikata, tare da raunata wasu da dama, a lokacin da suka kai farmaki kan wani filin hakar ma’adanai dake yankin Gurmana a karamar hukumar Shiroro.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Bayanai sun ce filin hakar ma’adanan da ‘yan ta’addan suka kai farmakin na karkashin kulawar wasu ‘yan kasar Sin.

Wani mazaunin yankin da jaridar Daily Trust ta zanta da shi, ya ce sun fuskanci tashin hankalin ne da tsakar ranar Larabar da ta gabata, inda suka afkawa shugabanni da masu aikin hakar ma’adanai ta hanyar budewa wuta kan duk wanda suka ci karo da shi.

Mutane fiye da 4 ake fargabar maharan sun sace, cikinsu kuwa har da ‘yan kasar China 4, kodayake har yanzu babu karin bayani a hukumance, zalika ba a kai ga tantance adadin mutanen da suka mutu a farmakin ba.

Jihar Neja ta dade tana fama da hare-haren ta’addanci daga bangaren wani tsagi na ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da suka balle, da kuma ‘yan bindiga da suka yi kaurin suna wajen kisa, da satar mutane domin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.