Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta yi bikin karrama sojoji 'yan mazan jiya

Najeriya ta yi bikin tunawa da kuma karrama sojojinta ‘yan mazan jiya, da sauran mutanen da suka sadaukar da ransu ga kasar a ranar Asabar, taron da ake yi a duk shekara, ranar 15 ga watan Janairu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mukarrabansa a birnin Abuja, yayin bikin karrama sojoji 'yan mazan jiya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mukarrabansa a birnin Abuja, yayin bikin karrama sojoji 'yan mazan jiya. © The Guardian Nigeria
Talla

Yayin Taron dai ana karramawa ta musamman ga wadanda suka yi yakin duniya na daya da na biyu, da kuma yakin basasar Najeriya.

A fadin duniya dai ana bikin tunawa da dakarun ‘yan mazan jiya ne da a ranar 11 ga watan Nuwamba na kowace shekara, ranar bikin tunawa da kawo karshen yakin duniya na farko.

To amma a Najeriya, an sauya ranar ce, saboda kawo karshen yakin basasar kasar da aka yi, bayan mika wuya da masu fafutukar kafa kasar Biafra suka yi a ranar 15 ga watan Janairu, na shekarar 1970.

A birnin Abuja, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci bikin, inda ya ajiye furannin karrama jaruman da suka rasu tare da duba faretin jami’an tsaro a babban dakin taro na kasar da ke Abuja.

Sauran manyan bakin da suka samu halartar bikin na tunawa da ‘yan mazan jiyan sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Tanko Muhammad, da kuma babban hafsan tsaro Janar Lucky Irabor.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.