Isa ga babban shafi
Najeriya

An hana zanga-zangar tunawa da yakin Biafra a Najeriya

Al’ummar Biafra da ke fafatukar ballewa daga Najeriya, sun bukaci jama’arsu da su zauna a gida a yayin bikin tunawa da yakin Biafra shekaru 50 da suka gabata.

An hana zanga-zangar tunawa da yakin Biafra saboda barazanar tsaro
An hana zanga-zangar tunawa da yakin Biafra saboda barazanar tsaro STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan jami’an ‘yan sanda sun ce, za su dauki mataki kan duk wata barazanar zaman lafiya a yankin.

Tuni dai aka rufe makarantun boko da coci-coci da ke yankin, yayin da bankuna suka ce, ba za su yi huldar kasuwanci da jama’a ba a yau, amma za su gudanar da aikinsu a cikin ofisoshinsu.

Tun a jiya ne mutane da dama suka kammala siyayyar kayayyakin masarufi bayan sun fahimci cewa, za a rufe kasuwanni a yau.

Rahotanni sun ce, an ga jiragen soji masu saukan ungula na ta shawagi a saman gidan shugaban Biafra Namndi Kanu.

Wasu rahotannin na cewa, manyan motoci 70 makare da sojojin Najeriya sun dauki hanyar zuwa Umuahia, mahaifar Nnamdi Kanu.

Mutanen Biafra dai sun yi shirin gudanar da zanga-zanga a wanann rana ta yau don tunawa da wadanda aka kashe a yakin, amma jami’an tsaro sun gargade saboda barazanar tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.