Isa ga babban shafi
Najeriya

Son zuciyar 'yan siyasa ne ya haddasa neman kafa Biafra - Shettima

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun zargi ‘yan siyasar yankin kabilar Igbo na kudu maso gabashin Najeriya da gazawa wajen samar da kayayyakin more rayuwa ga al’ummar yankin.

Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da aka kai a wata kasuwa.
Gwamnan Jahar Borno Kashim Shettima ya ziyarci wani a Asibitin Maiduguri wanda ya samu rauni a wani harin bom da aka kai a wata kasuwa. REUTERS/Stringer
Talla

Gwamnonin da suka ziyarci jihar Imo karkashin jagorancin Kashim Shettima, shugaban kungiyar gwamnonin arewacin kasar kuma gwamnan jihar Borno, sun danganta kokarin tada yamustin da kunngiyar IPOB mai neman kafa kasar Biafra ke yi, da yadda yankin ya tsinci kansa cikin koma baya.

Shettima, ya koka bisa yadda ya ce hanyoyi ko kuma titunan kasar basa cikin yanayi mai kyawu, duk da makudan kudaden da gwamnatin tarayya ke warewa a matsayin kason jihohin yankin na kudu maso gabashin Najeriyar.

Gwamnan ya kuma zargi 'yan siyasar kudu maso gabashin kasar da fifita cika aljhunansu, a maimakon bunkasa cigaban al'ummar yankin.

Tawagar gwamnonin wadda ta yi taro da shugabannin Hausawa da na Igbo a fadar gwamnatin Imo da ke Owerri, da fari sun fara ne da ziyartar Fatakwal, garin Umuahia da ke jihar Abia, duk a kokarinsu na dakile yiwuwar samun rikicin tsakanin wasu kungiyoyin yankunan kudancin Najeriyar da arewaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.