Isa ga babban shafi
Najeriya

An haramta kungiyar IPOB a Najeriya

GWAMNONIN Yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun bayyana haramta kungiyar nan ta IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra karkashin jagorancin Nnamdi Kanu. Matakin na zuwa a dai dai lokacin da rikici ke neman girmama a wasu yankuna na kasar duk dai kan bukatar kafa kasar ta Biafra.

Jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu.
Jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu. Reuters
Talla

Bayan wani zama da Gwamnonin suka gudanar yau a Enugu, Gwamnan Jihar Ebonyi, David Umahi ya ce sun cimma matsayar ne tare da shugabannin Yankin da Yan Majalisun Tarayya da suka fito daga Yankin da kuma shugabanin kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze.

Gwamnan ya ce daga yanzu duk wani korafi da jama’ar yankin ke da su, kai tsaye za su rika gabatarwa ga Gwamnonin su ko kungiyar ta Ohaneze ko ma Yan Majalisun Tarrayya daga Yankin.

Kafin dai daukar wannan mataki, rundunar sojin Najeriya ta sanar da haramta kungiyar wadda ta bayyana a matsayin ta yan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.