Isa ga babban shafi

Soyinka ya yi Allah wadai da kalaman Baba Ahmed

Fitaccen marubucin Najeriya, Farfesa Wole Soyinka, ya yi Allah wadai da kalaman Sanata Datti Baba Ahmed, ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar karkashin Jam’iyyar Labour a zaben da ya gabata a kasar. 

Fitaccen marubuci kuma masanin adabin Turanci a Najeriya, Farfesa Wole Soyinka.
Fitaccen marubuci kuma masanin adabin Turanci a Najeriya, Farfesa Wole Soyinka. AP - Themba Hadebe
Talla

Soyinka ya bayyana irin kalaman da Baba Ahmed ke yi a matsayin karan-tsaye ga bangaren shari’a da kuma tafarkin dimokradiyar Najeriya baki daya. 

Wannan ya biyo bayan kalaman ‘dan takarar yayin wata hira da tashar talabijin na Channels, inda ya bukaci shugaban kasar, Muhammadu Buhari, da alkalin alkalan Najeriya cewar kada su kuskura su rantsar da Bola Ahmed Tinubu, a matsayin zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu. 

Baba Ahmed ya bayyana cewar bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi da kuma gabatar masa da takardar shaida da hukumar INEC ta yi ya sabawa dokar kasa. 

Tuni Hukumar kula da kafofin yada labarai ta NBC ta ci tashar Channels tarar naira miliyan 5 saboda saba ka’idar aiki wajen bai wa Baba Ahmed, damar yin irin wadannan kalamai kai tsaye. 

NBC ta bayyana cewar kalaman na Baba Ahmed, na iya tinzira tashin hankali saboda haka ya saba ka’idar aikin jarida. 

Soyinka a sanarwar da ya gabatar ya kuma soki irin haren-haren da aka kai wa baki mazauna birnin Lagos lokacin zaben gwamnonin da aka yi. 

Marubucin ya kuma gargadi kafofin yada labaran Najeriya akan irin rahotanni da kuma hirarrakin da suke yi wadanda ke iya tada hankali, ko kuma gabatar da rahotanni da ba haka suke ba, wadanda yace ka iya ta da hankalin jama’a ko kuma tayar da tarzoma. 

Soyinka yace sau 3 yana aikewa da sakonni ga Peter Obi inda yake shaida masa cewar muddin ya fadi zabe to, ya zargi magoya bayansa, saboda irin matakan da suka dinga dauka kafin gudanar da zaben da akayi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.