Jami'an tsaron Najeriya sun kama 'yan daba da dama yayin zaben gwamnoni
Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun cafke mutane da dama da suka yi yunkurin haddasa rikici a yayin gudanar da zaben gwamnonin jihohi a sassan kasar, ciki har da Kano da Lagos.
Wallafawa ranar:
A jihar Kano kadai, jami’an ‘yan sanda sun kama jumillar mutane 161 da suka hada da wani dan majalisar jihar, Isyaku Ali-Danja bisa zargin su da kokarin haddasa hatsaniya a yayin da jama’a suka fito domin kada kuri’unsu a ranar Asabar.
Bayanai na cewa, dan majalisar mai wakiltar mazabar Gezawa, shi ne ya jagoranci ayarin ‘yan daba domin kai hari kan ofishin Hukumar Zabe ta INEC a Karamar Hukumar Gezawa.
Hakan nan a jihar Lagos da ke kudancin Najeriya, jami’an ‘yan sandan sun damke mutane 17 cikinsu har da wata mace guda bayan sun yi yunkurin tayar da hankali a yayin zaben.
‘Yan sandan na Lagos sun kuma yi nasarar kwato akwatinan zabe da wasu ‘yan jagaliya suka yi awon gaba da su.
A bangare guda, Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC sun kama akalla mutane 65 a sassan jihohin kasar 28 a yayin gudanar da zaben na gwamnoni saboda yadda suka yi ta rudar mutane da kudi suna saye kuri’unsu.
Jami’an na EFCC sun kwace wasu daga cikin kayayyakin sayen kuri’un kamar a jihar Sokoto, inda suka kwace turamen atamfa da aka yi ta raba wa mata a matsayin cin hanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu