Isa ga babban shafi

An girke karin Sojoji a sassan Lagos saboda fargabar barkewar rikici

Rahotanni daga birnin Lagos da ke kudancin Najeriya sun bayyana yadda aka girke karin jami’an tsaro a sassan jihar don kaucewa barkewar rikici bayan hare-haren da wasu ‘yan daba suka kai wa masu shaguna a kasuwanni da cikin anguwanni.

Jami'an tsaro na sintiri a birnin Lagos a yayin zaben Najeriya
Jami'an tsaro na sintiri a birnin Lagos a yayin zaben Najeriya © Taiwo Arifayan for RFI Hausa
Talla

Yankunan da aka girke jami’an tsaron sun kunshi Mushin da Ikeja da Ebute Meta da kuma Oshodi baya ga Cele da kuma anguwar Mile Two duk dai a yunkurin kaucewa samun rikici.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa daukar matakin girke jami’an tsaron da suka kunshi Sojoji da ‘yan sanda na da nasaba da fargabar da ake da it ana yiwuwar masu shagunan da ‘yan daba suka farmaka a jiya su iya mayar da martani.

Tun a jiya litinin wasu tsageru suka fara farmakar shagunan da ke unguwar Lagos Island da kuma kasuwannin Balogun da Mandilas wanda ke da nasaba da sakamakon zaben da ya nuna shan kayen Bola Ahmed Tunibu na jam’iyyar APC a jihar wadda ke matsayin gida gare shi.

Hatta zirga-zirgar ababen haw ana haya ta gamu da tangarda a sassan na Lagos saboda fargabar barkewar rikici.

Kakakin rundunar ‘yan sand ana jihar Lagos Benjamin Hundeyin ya yi gargadin cewa duk wani yunkurin wargaza zaman lafiya a sassan birnin zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Peter Obi na jam'iyyar LP ne dai ya lashe zaben jihar ta Lagos da gagarumin rinjaye fiye da takwarorinsa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da Bola Tunibu na APC.

Yanzu haka dai hukumar INEC na ci gaba da tattara sakamakon zabe inda Bola Tunibu ke jagoranci da kuri'u fiye da miliyan 6 da dubu dari 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.