Isa ga babban shafi
Zaben Najeriya na 2023

Sanwo-Olu ya yi tazarce a matsayin gwamnan Legas

An sake zaben Baba Jide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Legas.

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu LASG
Talla

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Mista Sanwo-Olu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Sanwo-Olu ya samu kuri'u 762,134 wajen doke manyan abokan hamayyarsa - Olajide 'Jandor' Adediran na PDP wanda ya samu kuri'u 62,449 da Gbadebo Rhodes-Vivour na jam'iyyar LP wanda ya samu kuri'u 312,329.

Baturen Zabe na INEC, Adenike Oladiji, wanda ya bayyana sakamakon zaben ta ce Mista Sanwo-Olu ya samu kashi 25 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada, sannan kuma shi ne ya fi yawan kuri’u a zaben don haka shi ya lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.