Isa ga babban shafi

Wanda ya yi kokarin kawo cikas ga zabe zai hadu da fushin doka-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi gargadi wadanda ke kokarin kawo cikas ga zabukan da ake shirin gudanarwa cikin shekara ta 2023 a kasar cewa lalle za su hadu da fushin doka.

President Buhari in Maiduguri
President Buhari in Maiduguri © Nigeria presidency
Talla

Shugaba Buhari ya yi wannan gargadi ne a jawabin da ya gabatar wa al’ummar kasar dangane da shiga sabuwar shekara ta 2023, yana mai kira ga illahirin ‘yan Najeriya da su tabbatar da wadannan zabuuka sun gudana a cikin yanayi na tsari, haske, ‘yanci da kuma mutunta doka.

Buhari ya ce watannin da ke gaba na da matukar muhimmanci ga gwamnatinsa, musamman a fannoni guda uku da suka hada da tsaro, tattalin arziki da kuma ci gaba da yaki da rashawa a duk fadin kasar.

A wani bangare na jawabinsa, Muhammadu Buhari ya ce ya zama wajibi ga ‘yan Najeriya su tabbatar da cewa ‘yan siyasa ba su yi amfani da su domin tayar da fitina a lokacin wadannan zabuka da take ba.

Shugaban ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da ya ce ya samu a cikin shekaru 7 da suka gabata, sannan ya ce yana murna ga wadanda ke yaba wa kokarin da ya yi da ma wadanda ke sukar salon mulkinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.