Isa ga babban shafi

Na yi iya ƙoƙari na a shugabancin Najeriya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace ya yi iya bakin kokarinsa a matsayinsa na jagoran kasar, lura da irin dimbin matsalolin da suka addabi kasar da kuma irin gudumawar da ya bayar a cikin shekaru sama da 7 da suka gabata. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron kasashen Afirka da Amurke da ke gudana a Washington DC na kasar Amurka . 14/12/22
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin taron kasashen Afirka da Amurke da ke gudana a Washington DC na kasar Amurka . 14/12/22 © Bashir Ahmad
Talla

Buhari yace Najeriya kasa ce babba, kuma mai yawan jama’a tare da tarin kalubale, amma hakan bai hana shi sauke nauyin da ya rataya akansa ba, a wasu bangarori a cikin wadannan shekaru 7 da rabi da ya yi yana jagorancin kasar. 

Shugaban yace magance matsalolin da suka addabi matasa shine babban aikin da gwamnatinsa ta saka a gaba, saboda alkawarin da ya musu na samar musu makoma mai kyau a shekaru masu zuwa. 

Gina matasa

Buhari ya bayyana muhimmancin gina matasa ta hanyar da zasu kaucewa tsatsauran ra’ayin addini da kuma nuna banbanci a tsakanin al’umma, batutuwa guda biyu da yace suna matukar illa a harkokin gina kasa. 

Shugaban ya yi wadannan kalamai ne a birnin Washington lokacin ganawa da shugabannin wata kungiyar da ake kira Abu Dhabi Forum wadanda suka hada da shugaban ta Sheikh Al Mahfoud Bin Bayyah da mataimakinsa Fasto Bob Roberts da suka ziyarce shi. 

Buhari ya jinjinawa shugabannin akan rawar da suke takawa wajen taimakawa matasa fahimtar juna da kuma alfahari da inda suka fito, matakin da yace zai taimaka wajen sanya su a turba mai kyau. 

Saura kasa da watanni hudu Buhari ya sauka

A watan Mayu mai zuwa shugaba Buhari zai bar ragamar mulkin Najeriya sakamakon kammala wa’adinsa na biyu, abinda zai kawo karshen mulkinsa na shekaru 8, yayin da za’a gudanar da zabe a watan Fabarairu domin zabo wanda zai maye gurbinsa. 

Najeriya mai dimbin mutanen da suka zarce miliyan 200 na ci gaba da fuskantar matsalolin ci gaba, yayin da matsalar tsaro ta yiwa kasar matukar illa a cikin shekaru sama da 12 da suka gabata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.