Isa ga babban shafi

Gazawar Buhari ta jefa 'Yan Najeriya cikin talauci - Gwamnoni

Gwamnonin Najeriya 36 sun shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar gazawarsa wajen samar da tsaro da kuma kasa cika alkawarin da ya yiwa ‘Yan Najeriya sune dalilan da suka jefa jama’ar kasar cikin halin kunci da rashin tabbas. Sanarwar da mai magana da yawun gwamnonin Abdurazaque Bello-Barkindo ya rabawa manema labarai tace abin takaici ne yaddda gwamnatin tarayya ke neman dorawa gwamnonin laifi dangane da irin talauci da halin kuncin da mazauna yankunan karkarar kasar ke fama da su. 

Wasu daga cikin Gwamnonin Najeriya
Wasu daga cikin Gwamnonin Najeriya © Premium Times
Talla

Gwamnonin sun ce a shekarar 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa ‘Yan Najeriya alkawarin cewar zai fitar da mutane miliyan 100 daga kamfen talaucin da ya addabi jama’a, amma ayau alkaluma sun nuna cewar ‘Yan Najeriya sama da miliyan 130 ke fama da talaucin inda suke rayuwa kasa da Dala guda kowacce rana kamar yadda ake kwatantawa a fadin duniya. 

Sanarwar tace a karkashin gwamnatin Buhari, an kwashe watanni kamfanin man NNPC ba ya iya zuba ribar da yake samu a asusun gwamnati, abinda ya tilastawa gwamnonin neman mafita ta wasu hanyoyi wajen samun kudaden shiga domin cike gibin kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya domin sauke nauyin dake kansu a bangare noma da raya karkara da ayyukan jinkai da kuma kula da lafiyar jama’a. 

Gwamnonin sun kuma cacaki ministan kasafin kudi Clement Agba wanda ya zargi gwamnonin da jefa mutane sama da kashi 72 a yankunan karkara cikin talauci da shara karya wajen kauda kan jama’a daga assalin abinda yake faruwa. 

Sanarwar tace abin sani shine, aikin farko da ya rataya akan gwamnatin tarayya shine kare lafiya da kuma dukiyoyin jama’a wajen samar da tsaro, domin aiwatar da harkokin ci gaba, amma abin takaici gwamnatin tarayya ta gaza a wannan bangaren, inda ta bar ‘Yan bindiga da ‘Yan ta’adda da kuma masu garkuwa da mutane suka mayar da kasar dandalin kashe jama’a da sace mutane a gidajensu da makarantu da kasuwanni da kuma gonaki. 

Gwamnonin sun ce tabbas gazawar shugaban kasaMuhammadu Buhari dake jagorancin gwamnatin tarayya ne ya haifar da dalilan kasa noma da samar da abinci da kuma harkokin kasuwaci a yankunan karkara, saboda yadda zaman lafiya ya gagara, abinda ya hana mutane zuwa gonakinsu da kuma kasuwanni. 

Wannan martini dai ya biyo bayan zargin da ministan kasafin kudi Clement Agba ya yiwa gwamnonin ne, inda yake cewa sun mayar da hankali wajen gina gadodin sama na motoci da filayen jiragen sama, maimakon bunkasa rayuwar jama’ar karkara. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.