Isa ga babban shafi

Yanzu magudin zabe na da matukar wahala a Najeriya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace magudin zaben da aka saba yi a shekarun baya ta hanyar sauya alkaluma na da matukar wahala, sakamakon yadda Hukumar zabe ta inganta tsarin zaben wajen amfani da na’urorin zamani. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kenan © Nigeria presidency
Talla

Yayin da yake ganawa da tawagar tsoffin shugabannin kasashen Afirka ta Yamma da suka ziyarci kasar domin ganin irin shirin da akeyi na gudanar da zaben shekara mai zuwa a karkashin jagorancin tsohon shugaban Saliyo, Ernest Bai Koroma, Buhari ya basu tabbacin cewar Najeriya zata gudanar da karbabben zaben da duniya zata amince da shi. 

Shugaban ya jinjinawa tawagar tsoffin shugabannin saboda matakin da suka dauka na yiwa Yankin Afirka ta Yamma aiki, yayin da ya bada misali da zabukan da akayi na baya bayan nan a Jihohin Anambra da Ekiti da kuma Osun, wadanda yace an baiwa jama’a damar zabin abinda suke so ba tare da musu katsalandan ba. 

Buhari yace Najeriya na samun ci gaba ta fannin dimokiradiya, kuma mutane na da damar zabin shugabannin da suke so, ba tare da la’akari da jam’iyya ba, saboda haka ba zasu bada damar amfani da kudi ko yan banga wajen tirsasawa masu zabe ba. 

Shugaban tawagar Ernest Bai Koroma ya jinjinawa shugaba Buhari saboda yadda yaki amincewa da bukatar wasu mutane na sauya kundin tsarin mulki domin sake takarar wa’adi na 3, sabanin abinda dokar kasar ta tanada, yayin da yace sauran kasashen Afirka na kallon Najeriya domin samun jagoranci. 

Koroma yace a lokacin da kasarsa ta Saliyo da Liberia suka fada cikin tashin hankali, Najeriya ce ta kai musu dauki domin dawo da zaman lafiya. 

Tsohon shugaban ya bukaci Buhari da ya duba wasu korafe korafen da yan siyasa keyi da suka hada da matsalar tsaro da kuma wadanda ke iya shafar kimar zaben. 

Daga cikin yan tawagar akwai tsohuwar mataimakiyar shugabar kasar Gambia, Fatoumata Tambajang da tsohon wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka ta Yamma, Mohammed ibn Chambas da kuma Ann Iyonu daga Gidauniyar Goodluck Jonathan. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.