Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta gargadi 'yan siyasa wajen amfani da 'yan banga

Gwamnatin Najeriya ta gargadi Gwamnonin Jihohin kasar 36 da su kaucewa yin amfani da 'yan bangar siyasa wajen hana abokan hamayyarsu gudanar da tarurrukan yakin neman zabe, musamman ganin lokacin zaben shekara mai zuwa na karatowa. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara akan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno ya gabatar da wannan gargadi, inda yake cewa an baza jami’an tsaro a fadin kasar domin murkushe duk wani yunkurin haifar da tashin hankali wajen zaben mai zuwa. 

Mongonu yace abin takaici ne yadda gwamnonin ke amfani da karfin mulki wajen tirsasawa abokan adawarsu, maimakon gabatar da ayyukan da suka yi domin janyo hankalin masu kada kuri’u su zabi wadanda suke marawa baya. 

Rahotanni sun ce jam’iyyun adawa na ci gaba da fuskantar matsaloli sosai wajen tallata yan takararsu ta hanyar manna fastoci ko ta kafofin yada labarai ko kuma gudanar da tarurrukan yakin neman zabe. 

A makwannin baya ne kwamitin wanzar da zaman lafiya dake karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranci jam’iyyun siyasar da kuma yan takarar sun a shugaban kasa wajen rattaba hannu akan yarjejeniyar kaucewa tashin hankali lokacin yakin zaben da kuma yayin gudanar da zaben. 

Har ila yau an gudanar da irin wadannan bukukuwan rattaba hannu a matakan jihohi domin tabbatar da cewar shugabanin siyasar da yan takara sun mutunta dokar kaucewa tashin hankalin ko tinzira magoya bayansu haifar da rigima. 

Sai dai rahotanni dake fitowa daga wasu jihohi na nuna yadda ake kaucewa yarjejeniyar wajen musgunawa jam’iyyun dake adawa da gwamnatin dake ci a matakan jihohin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.