Isa ga babban shafi

Ina kan baka na wajen ganin anyi zabe mai inganci badi - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake jaddada matsayin gwamnatinsa na ganin an gudanar da tsaftacacen zabe mai ingancin da duniya zata amince da shi a watan Fabarairu, duk da hare haren da batagari suke ci gaba da kaiwa a ofisoshin hukumar zaben kasar. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AP - Bayo Omoboriowo
Talla

Buhari ya shaidawa jami’an Cibiyar tabbatar da zaman lafiya dake Washington cewar, har yanzu yana kan bakarsa na ganin an samar da yanayi mai kyau da zai baiwa hukumar zaben damar gudanar da karbabben zabe a shekara mai zuwa. 

Ko a wannan mako sanda ‘Yan sanda sun bindige mutane 3 da suka kai hari Cibiyar hukumar zaben dake Jihar Imo, yayin da hukumar zaben ta kasa ta sanar da cewar a wannan shekara kawai an kaiwa ofisoshinta hare hare har sau 51. 

kayan zabe daga hukumar INEC a Najeriya
kayan zabe daga hukumar INEC a Najeriya Reuters

Shugaban Najeriya ya bayyana wadannan hare hare a matsayin tsiraru wadanda ba zasu iya shafar kimar zaben baki daya ba, yayin da yace an samu ingancin tsaro a wasu yankunan kasar. 

A shekara mai zuwa ake saran shugaba Buhari ya kawo karshen wa’adin mulkinsa na shekaru 8, abinda ke nuna cewar Najeriya zata samu sabon shugaban kasa daga cikin ‘yan takarar da suke ci gaba da karade sassan kasar domin neman goyan baya. 

Buhari na ziyarar Amurka ne a karkashin gayyatar shugaba Joe Biden domin halartar taron inganta dimokiradiya, yayin da Biden ya bukaci kasashe 6 na Afrika da zasu gudanar da zabe a shekara mai zuwa da su tabbatar da ganin an yi shi cikin kwanciyar hankali, bayan Amurka tayi alkawarin taimaka musu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.