Isa ga babban shafi

Najeriya: Jami'an tsaro sun kashe maharan da suka kaiwa INEC hari a jihar Imo

An kashe ‘yan bindiga uku da sanyin safiyar Litinin a lokacin da ‘yan sanda suka dakile wani hari da aka kai ofishin zabe a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

An kashe uku daga cikin maharan yayin da aka kama biyu daga cikin su.
An kashe uku daga cikin maharan yayin da aka kama biyu daga cikin su. © dailytrust
Talla

Harin da aka kai a babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (INEC) da ke Owerri, babban birnin jihar Imo, ya biyo bayan makamancinsa, yayin da kasa da watanni uku suka rage a gudanar da zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.

A watan Fabrairu ne ‘yan Najeriya za su kada kuri’a domin zaben wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda tsohon kwamandan sojojin kasar ne da zai sauka daga mulki bayan wa’adi biyu.

Hare-hare na baya-bayan nan da aka kai kan ofisoshin INEC, musamman a yankin Kudu maso Gabas inda kungiyoyin ‘yan aware ke fafutuka, da tashe-tashen hankula daga kungiyoyin masu aikata laifuka na kara nuna damuwa kan tashe-tashen hankulan zabe.

“Wasu ‘yan bindiga sun kai hari hedikwatar INEC da ke Owerri da sanyin safiyar Litinin, inda suka lalata wani bangare na ginin da wasu kayan aiki,” kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Michael Abattam ya shaida wa AFP.

Ya ce jami’an ‘yan sanda sun dakile harin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.

"An kashe uku daga cikin maharan yayin da aka kama biyu daga cikin su," in ji shi.

Kakakin hukumar ta INEC, Festus Okoye, ya tabbatar da tashin hankalin a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, inda ya kara da cewa babu wani muhimmin kayan zabe da aka lalata.

Ya ce wannan ne karo na uku da aka kai wa cibiyoyin hukumar a jihar Imo hari, cikin kasa da makonni biyu kenan bayan harin da aka kai ofishin Orlu da ofishin karamar hukumar Oru ta Yamma a farkon watan Disamba.

A baya-bayan nan ne dai hukumar zaben ta yi gargadin karuwar barazanar zafafa tashe-tashen hankulan yakin neman zabe gabanin zaben, inda ta ce ta bi diddigin hare-hare akalla 50 a cikin watanni biyun da suka gabata.

Kungiyar IPOB mai fafutukar neman a ware wa 'yan kabilar Igbo a yankin Kudu maso Gabas kasarsu, ta sha musanta cewa ita ce ta haddasa rikicin.

Fiye da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro 100 ne aka kashe tun farkon shekarar da ta gabata a hare-haren da aka kai musu, kamar yadda wata kafar yada labaran kasar ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.