Isa ga babban shafi

An sake kona ofishin INEC a Najeriya

Yayin da ake ci gaba da tinkarar zaben Najeriya a farkon shekara mai zuwa, wasu bata-gari da ba a iya tantance su ba, sun kai hari ofishin Hukumar Zabe da ke Jihar Ebonyi inda suka kona shi tare da kayayyakin aikin da ke cikinsa. 

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriya. AP
Talla

Kwamishinan wayar da kan jama’a na Hukumar Zaben, Festus Okoye ya sanar da wannan aika-aikar da ya ce wasu mutanen da ba a gano ko su waye ba, suka aikata a ofishin hukumar da ke Karamar Hukumar Izzi ta Jihar Ebonyi da misalin karfe 10 na safiyar Lahadin nan. 

Okoye ya ce kwamishinan zaben jihar Onyeka Ugochi ya tabbatar musu da aukuwar lamarin, wanda ya ce babu wani mutum guda da ya jikkata, sai dai ginin hukumar da kuma kayan aikinsu. 

Daga cikin kayan aikin akwai akwatunan zabe 340 da shingen kada kuri’a 10 da injin din bada wutar lantarki 14 da tankin ruwa da kujeru da kuma tarin katin zabe na jama’a wadanda ba su karba ba. 

Okoye ya ce wannan shi ne hari na 3 da aka kai wa ofishin hukumar zaben, bayan wadanda aka kai a jihohin Ogun da Osun a ranar 10 ga wannan wata. 

Makwanni biyu da suka wuce, majalisar tsaro ta Najeriya ta bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sandan kasar da Daraktan Hukumar DSS da su ba za jami’ansu domin kare ofisoshin hukumar zaben a sassan Najeriya.  

A shekara mai zuwa ne Najeriya ke gudanar da manyan zabukan da suka kunshi na shugaban kasa da gwamnonin jihohi 27 da Yan majalisun tarayya da na jihohi 36 da Abuja. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.