Isa ga babban shafi

An haramta wa 'yan Najeriya ziyartar Dubai

Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta sake haramta wa 'yan Najeriya ziyartar kasarta ba tare da bayyana dalilinta na daukar wannan tsauttsauran mataki ba.

'Yan Najeriya da dama na yawan ziyartar birnin Dubai domin shakatawa.
'Yan Najeriya da dama na yawan ziyartar birnin Dubai domin shakatawa. REUTERS - ABDEL HADI RAMAHI
Talla

Kasar ta sanar da haka ne a wata sanarwa da ta rarraba wa abokan huldar kasuwancinta daga Najeriya da suka hada da ejojin da ke samar wa 'yan kasar takardun bisa, matakin da ake ganin zai dada dagula rikicin diflomasiya tsakanin kasashen biyu.

Wannan na zuwa ne bayan 'yan makwanni da Hadaddiyar Daular Larabawa ta tsaurara matakan bayar da bisa ga sabbin bakin da ke marmarin shiga cikin kasar.

Sanarwar ta ce, hukumomin kasar sun soke daukacin bukatun neman takardun bisa daga 'yan Najeriya da wasu kasashen Afrika na bakaken fata.

Kazalika mahukuntan na UAE sun ce, ba za su mayar wa 'yan Najeriya kudaden da suka kashe ba wajen neman takardun bisar da suka soke, yayin da kawo yanzu suka ki bayar da dalilinsu na daukar matakin.

Ba a karon farko kenan ba da Hadaddiyar Daular Larabawa ke sanya jerin takunkumai kan 'yan Najeriya, al'amarin da ya dada cakuda huldar diflomasiyar da ke tsakaninsu.

'Yan Najeriya da dama da suka hada da 'yan kasuwa da 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati na yawan ziyartar Dubai domin shakatawa ko kuma harkar kasuwanci da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.