Bidiyon Boko Haram kan jirgin yakin Najeriya na kasar Syria ne - Bincike
Wani kwararre kan sha’anin tsaro dake kasar Sweden Hugo Kaaman, ya zargi kungiyar Boko Haram da sharara zuki ta malle, ta hanyar amfani da wani tsohon hoton bidiyo daga aka dauka a kasar Syria, domin ikirarin cewar it ace ta kakkabo jirgin yakin Najeriya da ya bace a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Yayin fashin baki kan lamarin Kaaman ya ce, bidiyon da kungiyar Boko Haram ta yada na wani jirgin yaki mai saukar ungulu ne da aka harbo cikin Syria a shekarar 2012.
Bidiyon da mai sharhi Hugo Kaaman ya bincika, wanda kungiyar Boko Haram ta yada tana ikirarin harbo jirgin yakin Najeriya da ya bace
Boko Haram just released a video claiming it shows a NAF jet shot down by the group. Looking at the video, it appears as if the jet explodes mid-air. However, this is not true. BH took a 2012 video showing a SyAAF helicopter exploding mid-air over Idlib and superimposed it. Weak pic.twitter.com/f6dNFJ5dXO
— Hugo Kaaman (@HKaaman) April 3, 2021
Da yammacin ranar Larabar da ta gabata, jirgin yakin Najeriya ya bace a Borno jim kadan bayan kai samame kan mayakan Boko Haram.
A ranar Alhamis kuma rundunar sojin saman Najeriya ta wallafa sunayen matukan jirgin da tacet ana kyautata zaton hatsari yayi.
Sai dai a ranar Juma’a kungiyar Boko Haram ta wallafa bidiyon dake nuna baraguzan jirgin yakin da tace mayakanta ne suka kakkabo, koda yake rundunar Sojin saman Najeriya ta yi watsi da ikirarin da tace babu gaskiya cikinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu