Isa ga babban shafi
Najeriya - Boko Haram

Sojin saman Najeriya sun musanta ikirarin Boko Haram na kakkabo jirginsu

Rundunar Sojin saman Najeriya ta yi watsi da rahotannin dake bayyana cewar kungiyar Boko Haram ce ta harbo jirgin yakin ta da aka bayyana bacewar sa kwanaki 3 da suka gabata.

Shugaban rundunar sojin saman Najeriya Air Marshal Isiaka Oladayo Amao
Shugaban rundunar sojin saman Najeriya Air Marshal Isiaka Oladayo Amao © NAF TWITTER
Talla

Sanarwar da Mai Magana da yawun rundunar sojin ya Edward Gabkwet ya gabatar tace babu gaskiya a hotunan bidiyon da kafofin sada zumunta da kuma wasu kafofin yada labarai ke yadawa.

Kakakin hukumar yace hotan bidiyon dake nuna jirgin na tarwatsewa a sama bayan ance an harbor shi ba gaskiya bane, domin babu yadda za’ayi jirgin sama ya tarwatse haka kamar yadda aka nuna a bidiyon kana kuma aga wasu sassan jikin sa kamar yadda ake yadawa babu abinda ya same su.

Gabkwet yace ba abin mamaki bane sanin halin kungiyar Boko Haram ta yi amfani da bacewar jirgin wajen daukar alhakin harbo shi, musamman yanzu da aka dakushe kaimin ta wajen kai munanan hare hare.

Kakakin sojin ya roki Yan Najeriya da suyi watsi da farfagandar da akeyi game da hadarin jirgin domin bada damar gudanar da bincike domin gano assalin abinda ya faru.

Rundunar sojin saman Najeriya ta yi watsi da ikirarin Boko Haram na harbo jirgin yakinta

Gabwet yace rundunar zata cigaba da hadin kai da sauran bangarorin sojin Najeriya domin aiwatar da manufofin ta na ganin bayan Yan ta’addan da suka addabi yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Boko Haram ta dauki alhakin kakkabo jirgin

A ranar Jumma'a Kungiyar Boko haram ta ce ita ce ta kakkabo jirgin yakin Najeriya wanda aka bayyana bacewar sa kwanaki biyu da suka gabata.

Mai Magana da yawun rundunar sojin saman kasar Edward Gabkwet ya gabatar da sunayen matuka jiragen guda biyu wadanda aka ce sun bata tare da jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.