Isa ga babban shafi
Najeriya-Maiduguri

Jirgin yakin Najeriya ya bace a yankin arewa maso gabas

Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce wani jirgin yakin kasar kirar Alpha-Jet ya bace a yayin da yake shawagi a sararin samaniyar yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikicin Boko Haram.

Wani jirgin yakin Najeriya.
Wani jirgin yakin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, daraktan sashin hulda da jama’a a na rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, y ace jirgin yakin ya bace ne a daidai lokacin da yake taimakawa dakarun rundunar sojin kasa wajen yakar kungiyar Boko Haram a jihar Borno a ranar Laraba.

Gabkwet ya kara da cewar tuni jami’an tsaro suka bazama wajen neman jirgin yakin da ya bace da misalin karfe 5 da mintuna 8 a ranar Laraba 31 ga watan Maris.

Wannan al’amari dai na zuwa ne, bayan kusan watanni biyu da aukuwar hatsarin wani jirgen yakin Najeriyar da ya fadi a kauyen Bassa dake wajen Abuja, yayin da yake kokarin komawa birnin tarayyar bayan fuskantar matsalar inji, inda sojojin sama 7 suka rasa rayukansu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.