Isa ga babban shafi
Najeriya

Jirgin sojin Najeriya ya rikito a filin jiragen sama dake Abuja

Wani jirgin sama kiran Boeing 350 mallakar sojin saman Najeriya ya fadi a tashar jiragen saman Abuja dauke da mutane 6 a cikin sa.

Jami'an agaji da sauran mutane a wurin da jirgin sojin saman Najeriya ya fadi yayin kokarin sauka a filin jiragen sama na birnin Abuja.  21/2/ 2021.
Jami'an agaji da sauran mutane a wurin da jirgin sojin saman Najeriya ya fadi yayin kokarin sauka a filin jiragen sama na birnin Abuja. 21/2/ 2021. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rahotanni sun ce babu mutum guda daga cikin jirgin da ya tsira da ran sa, yayin da ministan sufuri Hadi Sirika ke cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Ministan ta kafar twitter ya tabbatar da cewa jirgin da ake kira ‘King Air 350’ mallakar rundunar sojin Najeriya ya fadi ne kusa da wurin sauka a tashar jiragen saman Abuja bayan yayi korafi kan masalar injin akan hanyar sa ta zuwa Minna.

Sirika yace rahotannin da ya samu sun nuna cewar an samu rasa rayuka, amma ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalin su domin bada damar gudanar da bincike, yayin da ya bukaci addu’a ga wadanda suka mutu.

Rahotanni sun ce mutane 6 a cikin jirgin cikin su harda da matuak biyu lokacin da ya gamu da hadarin da misalin karfe 10 da minitina 48.

Kafofin sada zumunta sun nuna hotan jirgin lokacin da jami’an kashe gobara ke fesa masa ruwa, yayin da mutane suka taru kusa da wurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.