Isa ga babban shafi
Wasanni - Kano

Kano Pillars ta karbe jagorancin gasar Firimiyar Najeriya

Kano Pillars ta dare saman teburin gasar Firimiyar Najeriya da maki 30, bayan samun nasarar doke Kwara United da kwallaye 2-0 a ranar Laraba.

Tawagar 'yan wasan kungiyar Kano Pillars dake jihar Kano a Najeriya.
Tawagar 'yan wasan kungiyar Kano Pillars dake jihar Kano a Najeriya. © Kano Pillars FC
Talla

Yayin fafatawar ta jiya ‘yan wasan Pillars Usman Babalolo da Rabi’u Ali ne jefa kwallayen 2 a ragar Kwara United.

Kafin tayi tattaki zuwa wasan da ta sha kaye a Kano, Kwara United ce ke jagorantar gasar Fimiyar Najeriyar ta bana da maki 27 bayan wasanni 15.

Sakamakon wasan da Enugu Rangers za ta fafata da Katsina United ne zai fayyace ko Pillars za ta cigaba da zama jagorar Firimiyar ko kuma za ta koma mataki na 2.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.