Isa ga babban shafi
Wasanni - Kano

Mai horas da Kano Pillars ya ajiye aikinsa

Mai horas da Kano Pillars Bafaranshe Emmanuel Lionel Soccoia ya ajiye aikinsa watanni 5 bayan kulla yarjejeniyar shekara 1 da kungiyar a watan Oktoban shekarar 2020.

Tsohon mai horas da kungiyar Kano Pillars Emmanuel Lionel Soccoia da ya ajiye aikinsa bayan ikirarin karya ka'idar yarjejeniyar da ya rattabawa hannu.
Tsohon mai horas da kungiyar Kano Pillars Emmanuel Lionel Soccoia da ya ajiye aikinsa bayan ikirarin karya ka'idar yarjejeniyar da ya rattabawa hannu. © Kano Pillars FC
Talla

Tsohon kocin kungiyar Black Leopards dake Afrika ta Kudu, ya bayyana rashin cika masa wasu alkawura dake kunshe a yarjejeniyarsa da Pillars da kuma yi masa katsalandan cikin aikinsa a matsayin dalilan da suka sanya shi zabin ajiye aikin horas da kungiyar.

Lionel ya ce yanzu haka yana bin kungiyar ta Pillars albashin watanni 5 da yawansa ya kai dalar Amurka dubu 25. Zalika ya koka kan gazawar da kungiyar tayi wajen sama mishi takardar izinin zama domin aiki a Najeriya kamar yadda doka ta tsara, abinda ya sa ofishin jakadancin kasarsa Faransa ya nemi ya koma gida, kasancewar cigaba da zamansa a Najeriya ya saba ka’ida.

Sai dai jami’in hulda da kafafen yada labaran kungiyar ta Pillars Rilwanu Idris Malikawa ya musanta zargin kocin mai murabus na cewar ana yi masa katsalandan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.