Isa ga babban shafi
Amurka- Najeriya

Amurka: An kame 'yan Najeriya dake jagorantar kungiyar 'yan damfara

Mahukuntan Amurka sun sanar da kame wani gungun ‘yan damfara da mafi yawan wadanda ke tafiyar da shi ‘yan Najeriya ne, bayan da suka damfari mutane da kamfanoni miliyoyin kudade.

Mafi akasarin 'yan damfarar da aka kame 'yan Najeriya ne.
Mafi akasarin 'yan damfarar da aka kame 'yan Najeriya ne. AFP Photo/MOHD RASFAN
Talla

A jimilce mutane 80 ne ake zargi da hannu wajen aikata laifin na damfarar jama’a, kuma 14 daga cikinsu na zaune ne a Amurka.

Tuni dai jami’an tsaron Amurka a birnin Los Angeles suka kame 17 daga cikin ‘yan damfarar da a yanzu ake nema ruwa a jallo.

Ma’aikatar shari’ar Amurka tace adadin kudaden da gungun ‘yan damfarar suka yi awon gaba da su ya kai dala miliyan 40, kwatankwacin naira biliyan 14, da miliyan 468 kenan.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewar cikin ‘yan Najeriyar da aka kame akwai Valentine Iro da kuma Chukwudi Christogunus Igbokwe, wadanda aka samu akalla dalar amurka miliyan 6 cikin asusunsu, wanda bincike ya tabbatar da cewa, na gungun ‘yan damfarar ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.