Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar NLC ta yi barazanar sake shiga yajin aiki

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC, ta baiwa gwamnatin kasar wa’adin ranar 30 ga watan Disamba na 2018 da muke ciki, da ta fara aiwatar sabon karin albashi na naira dubu 30 ko kuma ta fuskanci fushin kungiyar.

Hoton shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC Ayuba Philibus Wabba yayin jagorantar wata zanga-zanga a birnin Abuja, Najeriya. 9/2/2017.
Hoton shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC Ayuba Philibus Wabba yayin jagorantar wata zanga-zanga a birnin Abuja, Najeriya. 9/2/2017. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

NLC tace matukar ba’a soma aiwatar ta sabon tsarin albashin ba, za su shiga yajin aiki na sai baba ta gani daga ranar 6 da watan Janairu a shekarar 2019.

Shugaban kwamitin yajin aikin na kungiyar ta NLC kwamrade Nasir Kabir a tattaunawar da ya yi da wakilinmu na Abuja Muhammed Sani Abubakar, ya ce da fari sun zaci cewa kin mako biyu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai mika rahoton hadin gwiwar gwamnati da na kungiyar Kwadagon kan karin albashin zuwa majalisa domin zama doka, amma abin ya gagara.

A cewar Kwamrade Nasir Kabir sun yi mamakin yadda gwamnatin tarayyar ta amince da yi wa ‘yan sanda karin mafi karancin albashi zuwa kusan dubu 90, amma karin da suke nema na dubu 30 ya faskara.

01:01

Muryar Kwamrade Nasir Kabir na kungiyar NLC kan barazanar shiga yajin aiki

Mohammed Sani Abubakar

Gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC, TUC da kuma ULC dai na neman karin mafi karancin albashin ma’aikata daga daga naira dubu 18 zuwa dubu 30 sai dai har yanzu an gaza cimma matsaya tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohin kasar.

A baya dai kan wannan bukata, gamayyar kungiyiyoyin kwadagon suka shiga yajin aiki, sai da daga bisani sun janye bayan tattaunawa da bangaren gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.