Isa ga babban shafi
Najeriya

Ko me ya sa Boko Haram ke zafafa hare-hare?

Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kaddamar da farmaki duk da cewa, gwamnatin Najeriya ta sanar da shirinta na shiga tattaunawar sulhu da mayakan. Ko a baya-bayan nan sai da kungiyar ta kai kazamin hari a sansanin soji da kuma wasu kauyuka da ke jihar Borno, in da ta kashe mutane akalla 20 tare da jikkata sama da 60.

Abu Musab Al-Barnawi da ke jagorantar tsagin kungiyar Boko Haram a Najeriya
Abu Musab Al-Barnawi da ke jagorantar tsagin kungiyar Boko Haram a Najeriya Guardian Nigeria
Talla

A ‘yan makwannin da suka gabata ne, Ministan Yada Labarai da Al’adu na Najeriya Lai Mohammed ya bayyana cewa, sama da shekara guda kenan da wakilan gwamnatin kasar suka gana da weakilan mayakan Boko Haram don cimma matsayar samar da zaman lafiya a kasar.

Kazalika shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya ce, gwamnatinsa a shirye take ta karbi mayakan na Boko Haram da suka amince su ajiye makamansu a yayin kabar ‘yan matan makarantar Dapchi 105 da kungiyar ta sako bayan ta sace su a fadarsa da ke birnin Abuja.

Sai dai duk da wannan sanarwa, mayakan sun kara kaimi wajen far wa jami’an tsaro da fararen hula musamman ganin abin da ya auku a jihar Borno a shekaran jiya, in da mayakan suka kashe mutane akalla 20 tare da raunata sama da 60.

Ko da dai wasu bayanai na cewa, ga alama gwamnatin Najeriya ta fi karkata hankalinta kan tsagin Abu Musab Al-Barnawi wajen tattaunawar, yayin da ake kyautata zaton tsagin Abubakar shekau ne ya kai farmakin na baya-bayan nan.

To ko shin Shekau din na zafafa harin ne don jefa fargaba tare da nuna wa Najeriya cewa, har yanzu da sauran karfinsa? duk da rahotannin baya da ke nuna cewa an kraya lagwansa?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.