Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

An sada Daliban Dapchi da iyayensu

Gwamnatin Najeriya ta mika Daliban Dapchi ga iyayensu da tsakar ranar yau Lahadi bayan ganawarsu da shugaban kasar Muhammadu Buhari. Tun bayan da Kungiyar Boko Haram ta sako 'yan matan ne a ranar Larabar makon jiya aka mika su ga Gwamnatin kasar bayan yi musu gwaje-gwajen lafiya.

Wasu Daliban Dapchi kenan lokacin da ake sada su da mahaifansu karkashin rakiyar dakarun sojin Najeriya.
Wasu Daliban Dapchi kenan lokacin da ake sada su da mahaifansu karkashin rakiyar dakarun sojin Najeriya. RFIHAUSA/Bilyaminu Yusuf
Talla

Daliban wadanda suka isa garin na Dapchi karkashin rakiyar Jami'an tsaro, tuni aka sada su da iyayensu wadanda ke cike da farin ciki.

Tun da safiyar yau ne dai daliban suka hallara a filin jirgin saman Abuja, yayinda daga bisani aka kwashe su zuwa jihar ta Yobe don sada su da iyayensu.

Al'ummar Dapchi dai na cike da farin ciki duk da cewa dai murna ta koma ciki ga wasu daga cikinsu bayan da har yanzu aka gaza gano keyar Leah Sharibu da aka yi rade-radin sakinta a jiya Asabar.

Leah Sharibu dai ita ce Daliba daya tilo data rage a hannun mayakan na Boko Haram wadda suka ce ba za su sake ta ba har sai ta karbi addinin Islama, ko da ya ke dai gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi kokarin kubutar da ita cikin salama kamar sauran takwarorinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.