Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta janye kalaman sakin Leah Sharibu

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta janye kalaman babban Sufeton ‘Yansandan kasar Ibrahim Idris da ke cewa dalibar Dapchi daya da ta rage a hannun Boko Haram ta na kan hanyar komawa gida.

Gwamnatin Najeriya dai ta sha alwashin ganin ta kubutar da Leah Sharibu ta hanyar laluma kamar takwarorinta sauran daliban na Dapchi.
Gwamnatin Najeriya dai ta sha alwashin ganin ta kubutar da Leah Sharibu ta hanyar laluma kamar takwarorinta sauran daliban na Dapchi. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A jiya Asabar ne babban sufeton ‘Yansandan na Najeriya ya ce ya janye batun ziyarar da zai kai Dapchi saboda yiwuwar sakin Leah Sharibu daliba daya da ta rage a hannun mayakan na Boko Haram.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Lahadi ta hannun kakakin rundunar Jimoh Moshood ta ce ba a fahimci kalaman babban sufeton ba, la’akari da yadda daruruwan al’ummar ta Dabchi suka rika dakon isowar Leah Sharibu.

A baya dai rahotanni sun ce Kungiyar ta Boko Haram ta ki sakin Leah Sharibu ne saboda kin amincewarta da karbar addinin Islama ko da ya ke dai Malaman addinin na Islama na ci gaba da sukar matakin inda suka ce babu hujjar tilastawa wani mahaluki karbar addinin na Musulunci.

Gwamnatin Najeriya dai ta sha alwashin ganin ta kubutar da Leah Sharibu ta hanyar laluma kamar takwarorinta sauran daliban na Dapchi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.