Isa ga babban shafi
Najeriya

Martanin 'yan adawa kan rangadin Buhari a jihohin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da rangadi a wasu jihohin kasar biyar da ke fama da matsalolin tsaro sakamakon rikicin Boko Haram da kuma hare-hare tsakanin manoma da makiya. To sai dai tuni masu hamayya da shugaban kamar gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose  ke fassara ziyarar a matsayin yakin neman zabe.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Haruna/Femi Adesina
Talla

Kamar dai yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ke cewa, daga cikin jihohin da Muhammadu Buhari zai ziyarta sun hada da Benue da kuma Zamfara, wadanda rikicin makiyaya da manoma ko kuma ‘yan fashi da makami suka haddasa asarar rayukan mutane masu tarin yawa.

A lokacin da ya ziyarci jihar Taraba a ranar Litinin da ta gabata, shugaban ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi nasarar cafke mutane da dama da ake zargi da hannu wajen tayar da hankali, tare da bayar da umurnin kama wadanda da ke rike da makamai ba a kan ka’ida ba.

Yanzu haka dai ana dakon isar shugaban a jihar Yobe, in da makwanni biyu da suka gabata ‘yan Boko Haram suka yi awon gaba da dalibai mata sama da 100 a wata makaranta, yayin da Muhammadu Buhari zai ziyarci Rivers, ita ma wata jihar a kudancin kasar da ke fama da irin nata ‘yan bindigar.

To sai dai masu adawa da shugaban kamar gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose na kallon rangadin a matsayin yunkurin farfado da martabarsa musamman a daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen zuwa zabe a shekara ta 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.