Isa ga babban shafi
Najeriya

Rikicin Mambila ya lakume rayuka fiye da na Zamfara-Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, yawan mutanen da aka kashe a rikice-rikicen Mambila da suka hada da rikicin makiyaya da manoma ya zarce adadin wadanda suka mutu a makamancin rikicin a jihohin Zamfara da Benue.

Shugaba Muhammadu Buhari a jihar Taraba
Shugaba Muhammadu Buhari a jihar Taraba thecable.ng
Talla

A yayin ganawa da al’ummar Fulani da sauran kabilun Mambila a birnin Jalingo a jiya Litinin, shugaba Buhari ya ce, yana da hanyarsa ta tattara bayanai game da dukkanin tashe-tashen hankula da kuma kashe-kashen da ake fama da su a sassan Najeriya.

Buhari ya ziyarci Taraba ne don jajanta wa gwamnatin jihar da iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yayin da ya koka kan zubar da jinin jama’a.

Buhari ya ce, kokarin samar da tsaro da zaman lafiya bai tsaya kan gwamnati kadai ba domin kuwa, kowa na da gudun mawar da zai iya bayarwa.

Kazalika shugaban ya yi alkawarin gano wadanda ke da hannu a rikicin don fuskantar hukunci.

Bayanan shugaba Buhari na zuwa ne bayan rahotanni sun ce, kimanin mutane 20 aka kashe a rikicin baya-bayan nan a Mambila tare da sace shanu sama da 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.